29 Agusta 2025 - 18:51
Source: ABNA24
Iraki: Ta Fara Daukar Tsauraran Matakai Kan Kungiyoyin Ta'adda

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki ta sanar da cewa ta kama wasu da dama daga cikin shugabannin wadannan kungiyoyi tare da hadin gwiwar hukumomin leken asiri.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya habarta cewa: ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Irakin ta sanar a yau Juma’a cewa ta fara daukar tsauraran matakan tsaro a kan fandararrun kungiyoyi masu akalar kasar.

Birgediya Janar "Miqdad Miri", darektan hulda da jama'a da yada labarai na ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraki, ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Al-Sumaria News Network cewa: Ma'aikatar harkokin cikin gida ta dauki muhimman matakai a yakin da ake yi da kungiyoyin ta’adda, an kuma ba wa cibiyoyi da dama, musamman ma hukumomin leken asiri, da su bi diddigin wannan batu.

Ya kara da cewa: Ana bin wannan lamari da gaske kuma an kama shugabannin wasu kungiyoyin. Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin bin wasu mambobin kungiyar.

Miri ya kuma jaddada cewa, kungiyoyi masu karkata akalar sun ragu, amma ana ci gaba da yaki da su da gaske daga ma'aikatar harkokin cikin gida, da tsaron kasa, da leken asiri da sauran hukumomin tsaron Iraki.

Ya bayyana cewa: Wadannan kungiyoyi suna da nufin ruguza ginshikin al'umma kuma a wannan fanni suna kokarin haifar da mummunan yanayi.

Miri ya karkare da cewa: Jami'an tsaron Iraki a dukkan bangarori za su ci gaba da kai munanan hare-hare kan wadannan kungiyoyi tare da fatattake su a duk inda suke.

...................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha